Isa ga babban shafi
Kamaru

Shekaru biyu Kamaru na tsare da Ahmed Abba wakilin RFI Hausa

Kungiyar ‘yan jaridu ta duniya Reporters Without Borders ta yi allawadai da ci gaba da tsare wakilin RFI Hausa Ahmed Abba wanda kotun sojin Kamaru ta yanke wa hukuncin shekaru 10 a gidan yari a watan Afrilu.

Kungiyar 'Yan Jaridu ta duniya  ta sake yin kiran gaggauta sakin dan Jaridar RFI Hausa Ahmed abba.
Kungiyar 'Yan Jaridu ta duniya ta sake yin kiran gaggauta sakin dan Jaridar RFI Hausa Ahmed abba. RFI-KISWAHILI
Talla

Bayan daurin shekaru 10, kotun Kamaru ta ci Abba tarar kimanin yuro 85,000.

A cikin wata sanarwa, sakataren kungiyar ‘yan jaridun Janar Christophe Deloire ya ce babu dalilin da za a ci gaba da tsare Abba.

A ranar lahadi ne ake cika shekaru biyu cur da tsare Ahmed Abba a Kamaru bayan zarginsa da alaka da kungiyar Boko Haram, laifin da babu hujjoji akan dan jaridar da ke aiko wa sashen Hausa na RFI da rahotanni daga yankin arewa mai nisa.

Abba ya shafe kusan shekaru biyu a tsare cikin yanayi na wahala da azabtarwa tun watan Yulin 2015 da aka kama shi a yankin arewa mai nisa, kafin kotu ta yanke ma sa hukunci.

Hukumomin RFI sun dade suna allawadai da kama ma'aikacin na sashen Hausa ba tare da Kamaru ta gabatar da hujjojin dalilin tsare shi ba.

Yanzu Kungiyar 'Yan Jaridun ta sake yin kiran gaggauta sakin dan Jaridar na RFI Hausa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.