Isa ga babban shafi
Afrika

Afrika ta zama mashayar miyagun kwayoyi

Hukumar yaki da masu sha ko fataucin miyagun kwayoyi ta Majalisar dinkin duniya ta ce nahiyar Afrika na ci gaba da kasancewa wata babbar matattara ta mashayar miyagun kwayoyi, kamar dai yadda rahoton hukumar mai kula da shiyyar Afrika ya nuna.

Hodar Iblis jibge a kasa
Hodar Iblis jibge a kasa REUTERS/Mariana Bazo
Talla

Rahoton wanda aka fitar a daidai lokacin da ake bukukuwan zagayowar ranar yaki da fatauci ko kuma amfani da miyagun kwayoyi a duniya ya ce, a nahiyar Afrika ne miyagun kwayoyin suka fi arha idan aka kwatanta da sauran nahiyoyi na duniya, abin da ke kara kwadaita wa jama’a yin amfani da su.

Ofishin hukumar mai kula da Afrika a birnin Dakar na Senegal, ya ce yayin da ake sayar da gram daya na hodar ibilis a kan jika biyu da rabi na cfa kwatankwacin Euro 4, ana sayar da shi ne akan Euro 80 a kasashen Turai.

Shugaban ofishin na Majalisar dinkin duniya a birnin Dakar, Pierre Lapaque ya ce, ana samun karuwar mashaya da kuma masu safarar miyagun kwayoyi a nahiyar.

A can baya dai wadanda ke taimaka wa dillalan miyagun kwayoyin ana biyan su ne da kudi tsaba, amma yanzu an koma biyan su da hodar ibilis.

Majalisar dinkin duniya dai ta ware ranar 26 ga watan Yunin kowace shekara domin yaki da masu fatauci ko kuma shan miyagun kwayoyi a duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.