Isa ga babban shafi
Nijar

Ana taron zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista a Nijar

Watanni 8 bayan zanga-zangar adawa da Mujallar Charlie, shugabannin al’ummar Musulmi da kirista sun soma taron tattauna tabbatar da zaman lafiya a kasar da kuma rawar da za su taka wajen dakile ayyukan Boko Haram na Najeriya da mayakan Jihadi a Mali da Libya.

Masallacin Birnin Niamey a Jamhuriyyar Nijar
Masallacin Birnin Niamey a Jamhuriyyar Nijar AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA
Talla

Mutane da dama dai sun mutu a tanzomar da ta barke a watan Janairu domin nuna adawa da Mujallar Charlie Hebdo ta Faransa da ta wallafa wani zanen da ta alakanta da Manzon Allah SAW.

An  kona wauraren ibadar kiristoci da makarantunsu musamman a biranen Damagaram da Yamai babban birnin Nijar.

An dade Kiristoci na zaman lafiya da musulmi masu yawa a Nijar.

Taron zai mayar da hankali wajen farfado da zaman lafiya tsakanin al’ummar Musulmi da kirista a kasar.

Sannan taron zai tattauna yadda mabiya addinan biyu zasu taimaka wajen dakile ayyukan Mayakan Boko Haram da ke barazana a Jihar Diffa da ke makwabtaka da Najeriya, da kuma mayakan Jihadi a kasashen Mali da Libya.

Zanen Mujallar Charlie dai ya haifar da zanga-zanga a kasashen Musulmi da dama

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.