Isa ga babban shafi
Wasanni

Griezmann yayi nadamar kin amsa tayin Barcelona - L'Équipe

Jaridar labarin wasanni ta L’ Equipe da ke Faransa ta rawaito cewa, dan wasan gaba na Atletico Madrid, Antione Griezmann ya soma kokarin sauya sheka zuwa Barcelona a karshen kakar wasa ta bana.

Dan wasan gaba na Atletico Madrid Antoine Griezmann.
Dan wasan gaba na Atletico Madrid Antoine Griezmann. Federico Gambarini / AFP
Talla

Rahoton ya ce wata majiya ta kusa da Griezmann ta bayyana cewa, dan wasan yayi nadamar yin watsi da tayin Barcelona na komawa gareta a farkon kakar wasa ta bana.

A shekarar bara, rahotanni suka tabbatar da cewa, Griezmann na gaf da komawa taka leda a Barcelona, amma daga bisani sai dan wasan ya sauya shawara, inda ya kara wa’adin yarjejeniya da kungiyarsa ta Atletico har zuwa shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.