Isa ga babban shafi
wasanni

Plateau United da Abia Warriors sun sha kashi

Kungiyar Kwallon kafa ta Heartland ta samu nasararta ta farko a cikin wannan sabuwar kakar bayan ta casa Plateau United da ci 3-0 a birnin Owerri a gasar firimiyar Najeriya.

Tawagar Plateau United
Tawagar Plateau United Pulse.ng
Talla

Ita ma Remo Stars ta bada mamaki domin kuwa ta doke Abia Warriors da ci 2-1 a Umauhia.

Ko a ranar Lahadi da ta gabata, Abia Warriors ta sha kashi a hannun Nasarawa United da ci daya mai ban haushi.

MFM ta Lagos kuwa, ta samu nasara akan Kwara United da ci 2-0 , yayin da Niger Tornadoes da Rivers United suka tashi kunnen doki 1-1.

A ranar Alhamis ne za a kece raini tsakanin Kano Pillars da Elkanemi Warriors a  birnin Maiduguri na jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.