Isa ga babban shafi
Wasanni

Alexander Arnold na Liverpool zai yi jinyar fiye da wata guda

Raunin Alexander-Arnold na Liverpool da zai kai shi fiye da wata guda ya na jinya zai zama babban kalubale ga Club din wanda dama tun kafin yanzu ya ke fama da matsalar karancin masu tsaron gida.

Raunin Alexandre Alex dai kari ne kan kusan 'yan wasan Liverpool 5 da yanzu haka ke fama da jinyar raunin da suka samu a wasanni daba-daban.
Raunin Alexandre Alex dai kari ne kan kusan 'yan wasan Liverpool 5 da yanzu haka ke fama da jinyar raunin da suka samu a wasanni daba-daban. Reuters/Ralph Orlowski
Talla

Arnord wanda ya gamu da raunin a gwiwa yayin atisaye gabanin wasansu da Brighton da suka yi nasara da kwallo guda da banza, ya samu damar doka mintuna 90 na wasan amma kuma daga bisani likitansa ya ce yana bukatar hutun akalla wata guda ko fiye.

Matukar dai Arnold ya haura wata guda hakan na nuna cewa ba zai taka leda a wasansu na farko da BayernMunich wanda za su karbi bakwanci cikin watan Fabarairu karkashin gasar cin kofin zakarun Turai ba, haka zalika zai rasa wasa da dama karkashin gasar Firimiya da Club din ke fatan lashewa.

Haka kuma raunin na Arnold kari ne kan jerin majinyatan da Liverpool ke da su a yanzu haka, inda har yanzu Joe Gomez bai kammala warwarewa ba bayan karayar da ya samu a tafin kafa cikin watan nan ko da dai ana sa ran Jame Milner ya iya taka leda a wasansu da Crystal Palace da za su karbi bakwanci a asabar mai zuwa.

Yanzu haka dai Fabinho mai rike tsakiya ana ganin shi zai ci gaba da tsaron gida kamar dai yadda ya yi a ranar Asabar sakamakon rashin lafiyar Joel Matip, Gomez da kuma Dejan Lovren yanzu kuma ga karin Georginio Wijnaldum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.