Isa ga babban shafi
wasanni

Ronaldo ya lashe wa Juventus kofinta na farko a 2019

Cristiano Ronaldo ya jefa kwallo daya tilo da ta bai wa Juventus nasara akan AC Milan a wasan karshe na gasar Super Cup da suka gudanar a birnin Jedda na Saudiya.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo REUTERS/Alberto Lingria
Talla

Ronaldo wanda ya koma Juventus daga Real Madrid a bara, ya jefa kwallon ne a minti na 61, abin da ya sa Juventus ta lashe kofinta na farko a cikin wannan shekara ta 2019.

An dai tayar da jijiyoyin wuya gabanin wannan wasa, in da Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta bukaci kungiyoyin biyu da su kaurace wa buga wannan wasa a Saudiya saboda zargin da ake yi wa kasar kan kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi, yayin da a gefe guda, hukumomin Saudiya suka ce za a takaita yawan matan da za su shiga filin wasan.

Kafofin yada labarai sun rawaito cewa, mata kimanin dubu 15 ne suka shiga filin wasan na Sarki Abdalla daga cikin jummular ‘yan kallo dubu 62.

Koda yake matan sun shiga ne tare da rakiyar muharramansu kamar ‘ya’yansu ko kuma ‘yayyansu maza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.