Isa ga babban shafi

Liverpool ta fice daga gasar Europa duk da nasara kan Atalanta

Liverpool ta fice daga gasar cin kofin Europa duk da nasarar da ta yi a wasan daren jiya inda ta doke Atalanta da kwallo 1 mai ban haushi, amma da ya ke tawagar Italiya ta doke yaran na Jurgen Klopp da kwallaye 3 da nema har Anfield a makon jiya, dole ya sanya Reds din komawa gida jiki a sanyaye.

Ɗan wasan Liverpool Virgil van Dijk, yayin wasansu da Atalanta.
Ɗan wasan Liverpool Virgil van Dijk, yayin wasansu da Atalanta. AP - Jon Super
Talla

Liverpool na ci gaba da ganin koma baya a kusan dukkanin gasar da ta ke ciki dai dai lokacin da ya rage kankanin lokaci mai horarwa Jurgen Klopp ya raba gari da kungiyar a karshen kaka.

Kasa da mako biyu da suka gabata, Liverpool na jagorancin teburin firimiya ne da karfin gwiwar iya kai labari yayinda ta ke da kyakkyawan fata karkashin gasar ta Europa da ta tsinci kanta ciki a wannan kaka bayan gaza samun tikitin gasar zakarun Turai a kakar da ta gabata, sai dai dukkanin fatan kungiyar ya gamu da tangarda.

Yayin wasan na jiya Mohamed Salah ne ya zurawa Liverpool kwallon daya tilo tun a minti na 7 da fara wasa a bugun fenaritin da Liverpool ta samu bayan ketar da aka yi wa Trent Alexandre Arnold, amma kwallon ba ta iya sauya sakamakon wasan ba.

Tawagar ta Jurgen Klopp, na ganin mummunar koma baya a cikin kwanaki 12 da suka gabata, inda ta yi canjaras da Manchester United ta kuma sha kaye a hannun Crystal Palace a gidanta dukkaninsu karkashin firimiyar Ingila gabanin dukan da Atalantar ta yi mata wanda ya zama tarihi mai cike da ban mamaki.

Yanzu haka Liverpool za ta karkata hankalinta ne kacokan ga gasar Firimiyar Ingila, gasar da yanzu haka Manchester City ke jagorancin teburinta da tazarar maki 2 tsakaninta da Arsenal da kuma Liverpool wadanda ke matsayin ta 2 da ta 3.

Liverpool wadda ta lashe Carabao a watan Fabarairu, za ta yi iyakar kokarinta wajen samarwa kanta mafita a wasanni 6 da suka rage mata a karkashin gasar ta Firimiya, inda za ta kara da kungiyoyin, Fulham da Everton da West Ham kana Tottenham sannan Aston Villa sai kuma ta karkare da Wolves.

Sai dai a bangare guda kungiyoyin Manchester City da Arsenal wadanda dukkaninsu suka fice daga gasar zakarun Turai a shekaran jiya, za su yi kokarin matsa kaimi don ganin sun lashe kofunan gasar da suka rage musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.