Isa ga babban shafi

Sevilla ta lashe kofin Europa bayan doke Roma a bugun fenariti

Sevilla ta doke Roma a bugun fenariti tare da lashe kofin Europa karo na 7 yayin wasansa karshe cikin daren jiya laraba a filin wasa na Puskas Arena da ke Budapest.

Tawagar kwallon kafar Sevilla bayan lashe kofin Europa.
Tawagar kwallon kafar Sevilla bayan lashe kofin Europa. AP - Petr David Josek
Talla

Tun farko Dybala ya fara zurawa Roma kwallonta a minti na 34 da taimakon Mancini amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Sevilla ta farke sakamakon kuskuren zura kwallon da Mancini ya yi a ragarsu, dalilin da ya sa kenan har aka kai karshen wasa ana kwallo 1 da 1.

Bayan karkare hatta karin lokacin da aka yi wa karawar ta jiya ne kuma aka tafi bugun fenariti wato daga kai sai mai tsaron raga, inda Sevilla ta zura kwallaye 4 cikin biyar da ta doka a bangare guda Roma ta iya zura kwallo 1 tare da barar da hudu.

Nasarar na nuna cewa kungiyar ta Spaniya zuwa yanzu ta lashe dukkanin wasannin karshe 7 da ta doka a gasar tun bayan jagoranci Kyaftin Jesus Navas da ya kai su ga lashe kofin na farko a shekarar 2006 lokacin da suka doke Middlesbrough.

Yanzu haka dai Sevilla ta samu gurbin samun damar taka leda a karkashin gasar cin kofin zakarun Turai duk da cewa ba ta kammala Laliga a sahun ‘yan hudun saman teburi ba.

Wannan ne dai wasan karshe na farko da Mourinho ya jagoranta ba tare da samun nasara ba, bayan kai Roma ga nasarar lashe kofin Europa Conference League a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.