Isa ga babban shafi

Roma da Sevilla za su hadu a wasan karshe na cin kofin Europa

Kungiyoyin kwallon kafa na Sevilla da ke Spain da kuma Roma a Italiya na shirin haduwa da juna a wasan karshe na gasar cin kofin Europa da zai gudana a Budapest ranar 31 ga watan da muke ciki na Mayu.

Manajan Roma Jose Mourinho bayan nasara a wasan gab da na karshe na gasar Europa kan Beyer Leverkusen da kwallo 1 mai ban haushi.
Manajan Roma Jose Mourinho bayan nasara a wasan gab da na karshe na gasar Europa kan Beyer Leverkusen da kwallo 1 mai ban haushi. AP - Gregorio Borgia
Talla

Sevilla dai ta samu damar kaiwa wasan karshen ne bayan doke Juventus da kwallaye 2 da 1 wanda ke nuna a jumulla sun tashi wasa 3 da 2 lura da yadda suka yi kunnen doki wato kwalli daya da daya a haduwarsu ta farko.

Wannan ne dai karo na 6 da Sevilla ke kaiwa wasan karshen da taimakon kwallayen daga ‘yan wasansa Suso da kuma Erik Lamela.

Haduwa Sevilla da Roma za ta kayatar matuka musamman lura da irin dagiyar da tawagar da Jose Mourinho ke nunawa a wannan kaka.

Yayin wasan na jiya dai Roma ta rike Leverkusen ta yadda aka tashi wasa babu kwallo dama kuma salon da Jose Morinhon ya so amfani da shi kenan lura da yadda ya ke da rinjaye a wasan farko da aka tashi Roma na da 1 Bayern Leverkusen na nema.

Bisa alkaluma dai Mourinho ya lashe dukkanin wasannin karshe 5 da ya yi jagorancisu ciki har da wasan karshe na barra da ya kai Roma ga lashe kofin Europa Conference League, wanda ke nuna cewa wasan karshen na wannan karon komai zai iya faruwa ganin yadda itama Sevilla ke ci gaba da nuna bajinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.