Isa ga babban shafi

Barcelona za ta koma doka Europa bayan ficewa daga gasar zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fice daga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai bayan shan kaye da kwallaye 3 da nema a hannun Bayern Munich yayin wasansu cikin daren jiya laraba wanda ya gudana a gidan Barca wato Camp Nou.

Barcelona ta sha kaye da kwallaye 3 da nema a hannun Bayern Munich wanda ya fitar da su daga gasar cin kofin zakarun Turai.
Barcelona ta sha kaye da kwallaye 3 da nema a hannun Bayern Munich wanda ya fitar da su daga gasar cin kofin zakarun Turai. AP - Emilio Morenatti
Talla

Ficewar Barca daga gasar na da nasaba da yadda Inter Milan ta yi naara a wasanta da kwallaye 4 da nema kan Viktoria Plzen inda ta kammala wasanninta na rukunin a matsayin ta 2 biye da Bayern lamarin da ya bata damar tsallakawa zuwa zagayen kungiyoyi 16.

Romelu Lukaku da ya shiga filin wasa daga baya ya ci kwallao a kusan karshen wasa, inda tun da farko Edin Dzeko ya ci kwallaye 2, bayan da Henrikh Mkhitaryan ya ci kwallon farko ta wasan.

Hakan na nufin cewa Barcelona ta kammala a matsayi na 3 a cikin rukunin da ta ke, batun da ke nuna cewa kungiyar ta Catalonia za ta sake fafataw a gasar Europa a kaka ta 2 a jere.

Barcelona ta gaza hana kwallaye daga Sadio Mane da Eric Maxim Choupo-Moting da Serge Gnabry shiga ragarsu, duk kuwa da cewa a gida suke wannan wasa a gaban dimbim magoya bayansu.

Tun gabanin kammala wasan na jiya kaso mai yawa na magoya bayan Barca sun fice daga fili, yayinda wasu masu hakuri daga cikinsu suka yi saura don ganin abin da zai ture wa buzu nadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.