Isa ga babban shafi
Wasanni

An zartas da hukunci mai tsauri kan tsohon shugaban kwallon Brazil

Wata Kotu da ke zama a Brooklyn da ke Amurka, ta zartas da hukuncin daurin shekaru hudu kan tsohon shugaban hukumar kwallon kafa na kasar Brazil Jose Maria Marin bisa samunsa da laifin cin hanci da Rashawa.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa na kasar Brazil Jose Maria Marin.
Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa na kasar Brazil Jose Maria Marin. REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Marin mai shekaru 86, na daga cikin wasu manyan jami’an hukumar FIFA guda bakwai da jami’an tsaro suka kama a wani Otal da ke birnin Zurich na Switzerland cikin watan Mayu na shekarar 2015.

An dai dauri Jose Maria Marin ne bayan samunsa da laifin karbar Rashawa daga wasu kamfanonin tallata wasanni, domin basu damar haska muhimman wasanni a matakin nahiya ko duniya kamar gasar cin kofin kasashen kudancin Amurka, wato "Copa America".

Bayaga daurin shekaru hudu, kotu ta koma yanka masa biyan tarar dala miliyan 1 da dubu 200 da kuma bashi umarnin mika mata dala miliyan 3 da kusan rabi na tsabar kudi ko kadarar da ya mallaka ba bisa ka’ida ba.

Wannan hukunci dai bangare ne na gagarumin binciken da aka kaddamar karkashin jagorancin Amurka, dangane da zarge-zargen aikata almundahana ko cin hanci da Rashawa a hukumar FIFA, yayin da Sepp Blatter ke jagorantarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.