Isa ga babban shafi
wasanni

Na ci Juventus kwallo mafi kayatarwa a tarihi- Ronaldo

Gwarzon dan kwallon duniya da ke take taka leda a Real Madrid, Christiano Ronaldo ya ce, kwallon da ya jefa a ragar Juventus a fafatawar da suka yi jiya, ita ce kwallo mafi kyau da ya zura a tarihinsa na taka leda.

Lokacin da Christiano Ronaldo ya jefe kwallo mai kayatarwa a ragar Juventus
Lokacin da Christiano Ronaldo ya jefe kwallo mai kayatarwa a ragar Juventus REUTERS
Talla

Kwallon ta gigita ‘yan kallo a Turin, in da hatta magoya bayan Juventus sai da suka mike tsaye don girmama Ronaldo saboda wannan cin da ya yi wa Gianluigi Buffon a wasan na dab da na kusan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai zagayen farko a Allianz.

Shi kan shi Buffon sai da ya cire safar hannunsa don jinjina wa Ronaldo mai shekaru 33.

Ronaldo dai ya ci kwallaye da dama masu kayatarwa a wasannin da ya buga a kungiyoyi da kuma kasarsa ta Portugal, amma dan wasan ya yi amanna cewa, kwallon da ya zura a jiya ita ce mafi kayatarwa.

Dan wasan dai ya tashi sama sosai, in da ya bada tazarar kusan mita 3, sannan ya doki kwallon ta bayansa.

Real Madrid ce  ta yi nasara da ci 3-0 a fafatawar, in da Ronaldo din ya zura kwallaye guda biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.