Isa ga babban shafi
wasanni

Kocin Juventus bai damu da caccakar da ake yi ba

Kocin Juventus Massimiliano Allegri ya jaddada cewa, ko kadan bai damu da caccakar da ake yi ma sa na gaza samun nasara akan Tottenham a fafatawar da kungiyoyin biyu suka yi a jiya a gasar cin kofin zakarun Turai, in da suka ta shi 2-2.

Massimiliano Allegri ya ce, ba dole ba ne Juventus ta kai matakin wasan karshe a gasar zaakarun nahiyar Turai ba
Massimiliano Allegri ya ce, ba dole ba ne Juventus ta kai matakin wasan karshe a gasar zaakarun nahiyar Turai ba Reuters/ Max Rossi
Talla

A martanin da ya mayar, Allegri ya ce, masu zaton Juventus za ta zura kwallaye hudu a ragar Tottenham a jiya, sun yi kuskure.

Kocin ya ce, duk dai gasar zakarun Turai na a matsayin wani buri da ake son cimma, amma samun nasara ba abu bane mai sauki, yayin da ya kara da cewa, bai zama dole kungiyar ta rika kai matakin wasan karshe a kowacce shekara ba.

Juventus ce dai ta fara zura kwallaye biyu a ragar Tottenham a cikin mintina 10 da saka wasan ta hannun Gonzalo Higuain, yayin da Hary Kane da Chritian Erikson suka barke a mintina na 35 da kuma 71.

Yanzu haka a ranar 7 ga watan Maris ne kungiyoyin biyu za su sake fafatawa da juna a zagaye na biyu na gasar a Wembley.

Ita ma dai Manchester City ta lallasa FC Basel da ci 4-0 a gasar ta zakarun Turai.

Wannan nasarar ta bai wa Manchester City kwarin gwiwar samun gurbi a matakin wasan dab da na karshe a gasar.

City ta jefa kwallaye uku a ragar Basel a cikin mintiuna 23 kuma dan wasanta Ilkay Gundogan ya taka rawar gani, in da ya zura kwallaye biyu daga cikin hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.