Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool ta hana Manchester City kafa tarihi

A karon farko kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta sha kashi a gasar firimiya ta Ingila a wannan kaka bayan Liverpool ta casa ta da ci 4-3 a fafatawar da suka yi a jiya Lahadi.

Sadio Mané na daga cikin wadanda suka ci wa Liverpool kwallaye a fafatawar
Sadio Mané na daga cikin wadanda suka ci wa Liverpool kwallaye a fafatawar Reuters/Carl Recine
Talla

Wannan rashin nasara ya kawo karshen burin Manchester City na kafa irin tarhin Arsenal wadda ta kammala kakar 2003-2004 ba tare da an doke ta ba.

Sai dai har yanzu Manchester City din ce ke jan ragama a teburin gasar da maki 62, yayin da Liverpool ta haye mataki na uku da maki 47, kamar yadda Manchester United da ke mataki na biyu ke da maki 47.

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya gargadi ‘yan wasansa da su dauki darasi daga abin da Liverpool ta yi musu, domin a cewersa, sun sakankance ganin cewa suna jan ragamar gasar ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.