Isa ga babban shafi
wasanni

Bercelona ta kammala cinikin Mina Yerri daga Palmeiras

Barcelona ta sanar da kammala cinikin mai tsaron baya, na kungiyar kwallon kafa ta Palmeiras Yerry Mina kan kudi Yuro miliyan 11 da dubu 800 a tsakar ranar yau Alhamis.

Barcelona ta gindaya ribar Yuro milyan 100 ga duk wani Club da ya bukaci sayen dan wasan kafin karewar kwantiraginsa na shekaru biyar.
Barcelona ta gindaya ribar Yuro milyan 100 ga duk wani Club da ya bukaci sayen dan wasan kafin karewar kwantiraginsa na shekaru biyar. REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Yerri dan Colombia mai shekaru 23 ya amince ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar tsakaninsa da Barcelona, duk da dai bata bayyana ranar da dan wasan zai sanya hannu ba.

Yerri dai shi ne dan wasa na biyu da Barcelona ta yi cinikinsa a wannan kaka bayan Philippe Coutinho da ta sayo daga Liverpool kan kudi Yuro milyan 160.

Tuni dai Barcelona ta gindaya ribar Yuro milyan 100 ga duk wani Club da ya bukaci sayen dan wasan kafin karewar kwantiraginsa na shekaru biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.