Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU na neman mafita kan kasafin kudi mai dogon zango

Jagororin Turai sun shiga rana ta biyu a babban taronsu a birnin Brussels, cikin wata tattaunawa mai sarkakiya don cimma matsaya kan kasafin kudin nahiyar na dogon zango da ya kai Yuro Tiriliyan daya.

Christine Lagarde, Ursula von der Leyen Charles Michel, David Sassoli, jiga - jigai a Tarayyar Turai.
Christine Lagarde, Ursula von der Leyen Charles Michel, David Sassoli, jiga - jigai a Tarayyar Turai. REUTERS/Johanna Geron
Talla

Taron da ake yi don samar da kasafin kudin nahiyar na shekaru 7, wanda shine na farko tun da Birtaniya ta fice daga kungiyar, ya bayyana yadda ake ci gaba da samun rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen Turai masu hannu da shuni da kuma wadanda ke rayuwa hannu baka hannu kwarya, inda yayin da wasu ke neman a yi tsumulmula tare da kaffa kaffa wajen kashe kudi, wasu kuma so suke a yi wa asusu wagegen kofa.

Dama dai gutsiri tsoma da murza gashin baki ba wani sabon abu bane a taron kungiyar irin wannan, sai dai wannan ya taho da nasa sarkkiyar ce sakamakon ficewar Birtaniya daga kungiyar.

Gibin da ficewar Birtaniya daga kungiyar ya samar ya kai na Yuro biliyan 75, la’akari da kasfin kudin shekarar 2021 zuwa 2027, amma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zake cewa ba hakan ne zai sa Tarayyar Turai ta rage buri da har zai sa ta dakile yawan kudin da take harin kashewa ba.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kashedin cewa akwai bambamce bambancen ra’ayi da dole sai an shawo kansu tsakanin kasashen.

Mai masaukin bakin taron, kuma shugaban majalisar zartaswar kungiyar, Charles Michel ya shafe tsawon lokaci yana tuntubar wakilai yana mai fatar gabatar da sabon kudiri a Juma’ar nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.