Isa ga babban shafi

Yajin aikin sufuri ya durkusar da tattalin arzikin Faransa

Wata kididdiga dangane da kalubalen da yajin aikin sufuri na fiye da watanni 3 ya haifarwa tattalin arzikin Faransa, ya nuna yadda tattalin arzikin kasar ya samu koma baya da fiye da kashi 1.2 cikin dari musamman a watanni ukun karshen shekara.

Masu zanga zanga da yajin aiki a Faransa
Masu zanga zanga da yajin aiki a Faransa REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Zanga-zangar hade da yajin aikin bangaren sufuri mafi tsawo da Faransa ta taba fuskanta a tarihi, kididdigar ta bayyana yadda kai tsaye ya yi mummunar illa ga tattalin arzikin kasar wanda ya fuskanci koma baya da kashi 1.2 cikin dari, musamman a watanni ukun karshen shekarar bara.

Rahoton Ofishin kididdiga kan hawa da saukar tattalin arzikin kasashen duniya, ya nuna koma bayar tattalin arzikin na Faransa a matsayin irinsa na farko tun bayan koma bayar watan Aprilu zuwa Yunin 2016.

Yajin aikin bangaren sufurin wanda ma’aikata suka shafe fiye da watanni 3 suna yi, don kalubalantar sabon shirin fanshon gwamnatin Macron kai tsaye da gurgunta shirin gwamnati na ganin kasar ta samu habakar tattalin arziki da akalla kashi 1.7 a karshen shekarar ta bara.

Gwamnatin Faransa wadda ta sha alwashin zabtare wani bangaren na harajin ‘yan kasar baya ga karin albashi ga wani kaso na ma’aikatan kasar musamman masu daukar karancin albashi don farantawa ko kuma kawo karshen zanga-zangar masu yaluwar riga da ke kalubalantar sauye-sauyen gwamnatin kasar musamman kan tattalin arziki da karin kudaden shiga, ta ce kai tsaye zanga-zangar sufurin ta gurgunta tsammaninta kan habakar da tattalin arzikin kasar zai yi.

Kazalika kididdigar ta nuna yadda aka samu koma baya hadda a hada-hadar kasuwanni baya ga gidajen cin abinci da Otel-Otel har ma da wuraren shakatawa na kasar, la’akari da yadda yajin aikin ya shafi zirga-zirgar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.