Isa ga babban shafi
Birtaniya

An fara yakin neman zabe a Birtaniya

An rusa Majalisar Dokokin Birtaniya gabanin zaben gama-gari da zai gudana a ranar 12 ga watan Disamba mai zuwa, yayin da a hukumance, jam’iyyun siyasar kasar suka kaddamar da yakin neman zabe.

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson REUTERS/Hannah McKay
Talla

Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya bukaci gudanar da zaben gaggawa da zummar kawo karshen kiki-kakar batun ficewar kasar daga gungun kasashen Turai.

A cewar Johnson, wannan kiki-kakar ta sama da shekaru uku, ta gurgunta Birtaniya kuma hakan ya fara yin illa ga kwarin guiwar da ake da shi a kasar wadda ita ce ta biyar mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Mr. Johnson ya gana da Sarauniya Elizabeth gabanin kaddamar da yakin neman zabensa, a yayin da kuma Ministansa na Wales Alun Cairns ya yi murabus bayan an zarge shi da sharara karya game da wani batu da ya shafi fyade.

Alkaluma sun nuna cewa, jam’iyyar Conservative ta samu tagomashi a daidai lokacin da aka fara yakin neman zaben, inda ta sha gaban babbar abokiyar hamayyarta, wato jam’iyyar Labour da kashi 7-17.

Sai dai masu tantance kuri’ar jin ra’ayin jama’a, sun gargadi cewa, tagomashin Conservative na raguwa saboda batun Brexit.

Mr. Johnson dai na ci gaba da kokarin shawo kan al’ummar kasar domin samun goyon bayansu dangane da ficewarsu daga Kungiyar Tarayyar Turai, yayin da ya ce, shugaban jam’iyyar Labour, Jeremy corbyrn zai haifar musu da tarnaki a fafutukarsu ta ficewar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.