Isa ga babban shafi
Faransa

Maharin birnin Lyon ya amsa laifinsa

Bayan shafe awanni 48 ya shan tambayoyi daga jami’an tsaron kasar Faransa, matashin da ke tsare bisa zarginsa da hannu a harin bam da ya jikkata mutane 13 a birnin Lyon ya amince da zargin da ake masa, tare da fayyace yadda ya shirya harin.

Wasu jami'an tsaron Faransa da ke sintiri a yankin birnin Lyon da bam ya tarwatse.
Wasu jami'an tsaron Faransa da ke sintiri a yankin birnin Lyon da bam ya tarwatse. France 24
Talla

Matashin mai shekaru 24, wanda kuma dalibi ne da ke nazari kan fasahar sadarwa, y ace tabbas shi ne ya hada bam din da ya dasa, kuma ya soma shirya kai harin ne, makwanni da dama da suka gabata.

Maharin ya kara da cewa a watannin Maris da kuma Afrilu ya sayo kayayyakin da ya hada bam din, inda kuma yayi ikirarin cewa shi kadai ya shirya kai harin na birnin Lyon ba tare da taimakon kowa ba, sai dai matashin ya amincewa cewa yana da alaka da kungiyoyn da suka saba kai makamantan hare-haren, ta hanyar bibiyar ayyukansu, ikirarin da yan sanda suka tabbatar, bayanda suka bincika na’urar komfutarsa ta tafi da gidanka.

A ranar Talata, jami’an tsaron Faransa suka kama wasu mutane 4 da ake zargin cewa suna da hannu wajen dasa bam din da ya jikkata mutane a birnin Lyon da ke kudu maso gabashin kasar.

Sai dai da fari jami’an tsaron sun cafke matashin dan kasar Algeria da a yanzu ya amsa laifinsa ne.

A baya dai kungiyar IS ta sha yin ikirarin kai hare-hare a sassan nahiyar Turai ciki har da Faransa, sai dai a wannan karon har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin na birnin Lyon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.