Isa ga babban shafi
Faransa

Yan sandan Faransa sun cafke mutane 4 kan harin birnin Lyon

Jami’an tsaron Faransa sun kama mutane 4 da ake zargin cewa suna da hannu wajen dasa bam din da ya jikkata mutane 13 karshen makon da ya gabata a birnin Lyon da ke kudu maso gabashin kasar.

Yankin birnin Lyon da bam ya tarwatse.
Yankin birnin Lyon da bam ya tarwatse. AFP / PHILIPPE DESMAZES
Talla

Da fari dai jami’an tsaro sun cafke wani mutum guda ne dan kasar Algeria, daga bisani kuma suka kai samame kan wani gini, inda suka cafke sauran wadanda ake zargin.

Mutane 13 da suka jikkata a harin bam din na birnin Lyon sun hada da mata 8, maza 4 da kuma wata karamar yarinya mai shekaru 10.

A baya dai kungiyar IS ta sha yin ikirarin kai hare-hare a sassan nahiyar Turai ciki har da Faransa, sai dai a wannan karon har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin na birnin Lyon.

Hukumomin tsaron Faransa dai sun dade cikin shirin ko ta kwana, tun bayan harin da aka kai a birnin Paris cikin shekarar 2015, wanda aka hallaka sama da mutane 250.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.