Faransa ta sake garkame Kwamandan Al'Qaeda a gidan yari
Jami’an tsaron Faransa sun sake garkame daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Al-Qa’eda Peter Cherif a gidan yari bayan shafe shekaru 7 suna farautarsa, wanda kuma sauran hukumomin nahiyar Turai ke nemansa ruwa a jallo.
Wallafawa ranar:
Tun a shekarar 2011 jami’an tsaron Faransar ke neman Peter Cherif mai shekaru 36, bayan da ya tsere daga kasar a ranar da ake shirin yanke masa hukunci a Paris, kan zama mayakin Al’Qaeda a Iraqi cikin shekarar 2004, inda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 5.
A ranar 16 ga watan Disamban da muke ciki, jami’an tsaro suka kama Cherif a Djibouti bayan da ya shiga kasar da katin shidar jabu.
Peter Cherif mai shekaru 36 ya taka rawa wajen kisan ma’aikatan mujallar nan ta Cherlie Hebdo a 2015, daga bisani kuma ya zama babban kwamandan mayakan Al’Qaeda a Yemen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu