Isa ga babban shafi
Turai

Yawan wadanda ke neman barin Birtaniya zuwa Jamus ya karu

Jikokin yan gudun hijirar Birtaniya da suka tsere daga Jamus a lokacin mulkin Nazi, sun soma fafutukar ganin an maido musu da shaidar zama yan kasa a Jamus, don cigaba da kasancewa karkashin al’umar Kungiyar Kasashen Turai EU, bayan ficewar Birtaniya daga cikinta.

Saruruwan 'Yan uwan al'ummar Birtaniya da suka tserewa Jamus a zamanin mulkin Nazi sun soma neman komawa kasar ta Jamus.
Saruruwan 'Yan uwan al'ummar Birtaniya da suka tserewa Jamus a zamanin mulkin Nazi sun soma neman komawa kasar ta Jamus. YouTube
Talla

Rahotanni sun tabbatar da cewa yawan wadanda ke neman zama a Jamus yanzu haka ya ninka har sau 40, idan aka kwatanta da karshen shekarar 2016, wannan na zuwa ne tun bayan Birtaniya ta kada kuri’ar ficewa daga cikin Kungiyar Tarayyar Turai a watan yuni na shekara ta 2016.

A shekarar 2015, kididdiga ta nuna cewa jamus ta karbi bukatun neman fasfonta 43 ne kawai, saidai adadin ya haura zuwa 684 a shekarar 2016, inda daukacin su suka mika bukatar ta samun fasfon bayan Britaniya ta kada kuri’ar ficewa daga kungiyar.

Bayanan da ma'aikatar cikin gidan Jamus ta fitar sun nuna cewa, a shekarar da ta gabata, adadin masu bukatar ya sake haurawa zuwa 1,667.

Gwamnatin jamus dai, ta ce mafi akasarin mabukatan sun hada da yahudawa da kuma mambobin jami’yyun siyasa dokar Jamus dai ta baiwa ‘ya’ya da jikokin wadanda aka kashe ko azabtar, da har ta kaisu ga tserewa daga kasar a lokacin mulkin Nazi, damar sake neman izinin zama yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.