Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya amince da murabus din Ministan Cikin Gida

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amince da takardar marabus da Ministan Cikin Gidan kasar Gerard Collomb ya gabatar, bayan da farko ya ki amincewa ministan ya sauka daga mukaminsa kamar yadda ya bukata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Ministan Cikin Gida Gérard Collomb a Paris
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Ministan Cikin Gida Gérard Collomb a Paris CHRISTIAN HARTMANN/AFP
Talla

A ranar Litinin da ta gabata ne Collomb ya gabatar da takardarsa ta marabus, to sai dai shugaba Macron ya ki amincewa da ita, to amma duk da haka, ministan mai shekaru 71 a duniya ya ci gaba da tsayawa a kan bakarsa.

Makusantan shugaban kasar sun ce, Macron ya bi dukannin matakan da suka dace domin rarrashin ministan amma ya ki, in da daga karshe ya bukaci Firaminista Edouard Philippe ya ci gaba da rike ma’aikatar a matsayin rikon kwarya har zuwa lokacin da za a nada sabon minista.

Mista Collomb ya ce, ya yi marabus ne don tsayawa takarar neman mukamin magajin garin birnin Lyon a shekara ta 2020, to sai dai manazarta na kallon ficewarsa daga gwamnati a matsayin babban koma-baya ga shugaba Emmanuel Macron, kasa da watanni biyu da ministan muhalli Nicolas Hulot ya yi murabus.

Tun lokacin da aka nuna dogarin shugaba Macron mai suna Alexender Benalla na dukan masu zanga-zanga a wani hoton bidiyo ne, aka fara samun tsamin danganta tsakanin ministan da kuma fadar shugaban kasar.

Ministan Cikin Gida na da matukar muhimmanci sosai a Faransa, musamman lura da yadda kasar ke kara fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda tun 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.