Shugabanin Turai na taro don cimma matsaya kan batun bakin-haure
A yau Lahadi Shugabanin kasashen Turai 16 za su gudanar da taron su a Bruxos domin fayyace daya bayan daya hanyoyin warware batun yan ci’rani dake kokarin haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Faransa ta bukaci a samar da wasu cibiyoyi a Italiya da Spain da za su mayar da hankali domin tanttance ta yada za a iya samarwa yan ci’rani wurare zuwa kasashen da ya dace .
Sai dai Italiya ta bakin ministan cikin gidan ta, ta bayyana adawa, Ministan kasar ya bukaci Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya daina babakere dangane da batun yan ci’rani, Ministan ya bayyana cewa Faransa tana ina a lokacin da jirgin ruwan nan Aquarius ya ja dogon lokaci saman teku kafin Spain ta amince karbar yan ci’ranin a kasar ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu