Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta mutunta ka'idar EU kan kasafin kudi

A karon farko cikin shekaru 10, Faransa ta mutunta ka’idojin Kungiyar Tarayyar Turai na takaita kashe kudade, in da ta samu gibin kasafin kudi na 2017 kasa da hasashen Kungiyar.

Hukumar Kididdiga ta Faransa
Hukumar Kididdiga ta Faransa AFP PHOTO / THOMAS SAMSON
Talla

Hukumar Kididdiga ta Faransa, INSEE ta rawaito cewa, gibin kasafin da aka samu ya yi dai dai da kashi 2.6 a ma’aunin tattalin arziki na GDP a bara, abin da ya saba da hasashen EU na samun kashi 2.9.

Kazalika alkaluman da aka tattara na gibin kasafin 2017 sub yi matukar kasa fiye da na shekarar 2016, in da aka samu kashi 3.4.

Wannan dai na a matsayin labarin tattalin arziki mai dadi ga shugaba Emmanuel Macron da ya karbi ragamar kasar a cikin watan Mayun bara.

Ko da dai tun a lokacin tsohuwar gwamnatin gurguzu ta Francois Hollande aka fara yunkurin takaita kashe kudaden, amma jinjinar ta gwamnatin shugaba Macron ne.

Ministan Kudin Faransa, Bruno Le Maire ya ce, sun mutunta hidimarsu, in da yake cewa, wannan hujja ce da ke nuna cewa matakan da gwamnatin Macron ta dauka kan takaita kashe kudin nada tasiri.

Gabanin wannan tagomashi dai, Faransa ta shafe tsawon shekaru 10 ta na gaza mutunta ka’idojin Kungiyar Tarayyar Turai na takaita gibin kasafin, in da ta ke zarce kashi 3 da aka sanya a matsayin maki na ka’ida ga kowacce mamba a nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.