Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya ta kori jami'an Diflomasiyyar Rasha 23

Firaministan Birtaniya Theresa May ta sanar da Korar jakadun Diflomasiyyar Rasha 23 tare kuma da soke wasu tarin kwangiloli da ta bai wa Rashan ciki har da wadanda suka shafi gasar cin kofin duniya ta bana.Matakin Birtaniyar ya biyo bayan zargin da ta ke kan Rashar da hannu tsundum a yunkurin kisan wani tsohon jam’in leken asirinta Mr Sergei Skripal da ‘yarsa. 

Firaministar Birtaniya Theresa May yayin jawabin da ta gabatar gaban majalisar dokokin kasar da ya kai ga sallamar jami'an diflomasiyyar Rasha 23 a yau Laraba 14 ga watan Maris shekarar 2018.
Firaministar Birtaniya Theresa May yayin jawabin da ta gabatar gaban majalisar dokokin kasar da ya kai ga sallamar jami'an diflomasiyyar Rasha 23 a yau Laraba 14 ga watan Maris shekarar 2018. Reuters
Talla

Firaministar Birtaniyar Theresa May ta gabatar da jerin matakan yanke dangantaka da Rasha a jawabin da ta gabatar a zauren majalisar kasar da tsakar ranar yau Laraba.

Cikinj jerin matakan yanke hulda da Rashan baya ga korar jami'an Diflomasiyyar 23 akwai kuma basu wa'adin kwanaki 7 su kammala ficewa daga kasar, yayinda a banagre guda kuma za ta mika batun ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya don tattaunawa tare da daukar matakin gaba.

Tun a ranar hudu ga watan Maris ne aka yi yunkurin hallaka Sergei Skripal tare da ‘yar sa ta hanyar amfani da wata nau'in guba a birtaniyar, matakin da Birtaniyar ke ganin akwai hannun Rasha karara duk da cewa dai ta sha musanta hakan a baya.

A cewar Theresa May yayin jawabin da ta gabatar gaban zauren majalisar dokokin kasar,  Rashan ta gaza taimakawa da bayanai da Birtaniyar ta nema kan yadda aka yi amfani da nau'in gubar Novichok a garin Salisbury, don yunkurin hallaka Mr Sergei.

A baya dai Rashan ta ce a shirye ta ke ta bayar da duk wasu bayanai da ake bukata don bankado asirin wadanda ke da hannu a yunkrin kisan tsohon dan leken asirin wanda masanin kimiyya ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.