Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta dakile hare-haren ta'addanci 2 a bana

Gwamnatin Faransa ta sanar da dakile akalla hare-haren ta’addanci biyu da aka shirya kai wa kan jami’an sojinta da kuma babbar tawagar ‘yan wasanta cikin shekarar nan.Ministan harkokin cikin gida na Faransar Gerrard Collomb ya ce kasar na ankare da hare-haren da ake shirye-shiryen kai mata a tsawon shekaru 3 da suka gabata.

A cewar Gerard Collom ko a bara sai da Faransar ta dakile akalla hare-haren ta'addanci 20.
A cewar Gerard Collom ko a bara sai da Faransar ta dakile akalla hare-haren ta'addanci 20. REUTERS/Charly Triballeau/Pool
Talla

A cewar ministan harkokin cikin gidan na Fransa, Gerard Collomb daga watan Janairu zuwa yanzu akwai hare-hare 2 da ‘Yan ta’adda suka shirya kai wa wasu sassan kasar, kuma tuni asirinsu ya tonu yayinda ake shirye-shiryen zartas musu da hukunci.

Mr Collomb ya ce ‘yan ta’addan sun shirya kai hari na farko a yankin yammacin kasar da suka shirya kaiwa kan wata tawagar ‘yan wasa da galibinsu matasa ne, sai kuma na gabashin kasar da aka shirya kai wa kan jami’an tsaron kasar.

Ministan ya ce jami’an ‘yan sanda na ci gaba da bibiyar batun yayin da suke kame duk wadanda su ke da hannu kan shirin don yi musu hukunci.

A cewarsa ko a shekarar 2017, sai da kasar ta dakile shirye-shiryen harin ta’addanci har guda 20.

A shekarar 2015 ne wasu jerin mummunan hare-haren ta’addanci a Faransar ya hallaka akalla mutane 130, yayin da a watan Janairun shekarar wasu ‘yan ta’adda suka hallaka akalla mutane 11 a wani harin bindiga.

Ko a bara ma dai wasu hare-haren ta’addanci biyu sun hallaka mutum uku a kasar da na watan Aprilu da kuma na Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.