Kungiyoyin ma’aikata na bore kan kai wa gandirebobi hari a Faransa
Kungiyoyin da ke hankoron ganin an kyautata tsaro ga ma’aikata a Faransa, sun yi amfani da katakai da tayoyi wajen toshe hanyar shiga gidan yarin Vendin-le-Vieil, domin nuna fushin su, bayan da wani da ake tsare da shi ya far ma gandirebobi a makon da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin ma’aikata guda 3 ne suka bayar da sanarwa bayan kamala wani taro inda suka bayyana cewa ba a dauki wani matakin a zo a gani ba game da bukatun da suka gabatar, musamman a game da maganar tsaron lafiyar ma’aikata a wuraren ajiye masu laifi.
Daya daga cikin 'ya'yan wata kungiyar kwadago a kasar ya shaida wa manema labarai cewa ba za su bar kowa ya shiga cikin gidan yarin ba.
A wannan talata ake sa ran ministan shari’a na kasar ta Faransa Nicole Belloubet ya ziyarci gidan yarin domin duba yanayin al’amura.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne wani da ake tsare da shi bisa laifin ta’addanci ya far ma ma’aiktan gidan yarin Venddin-le-Viel, inda ya raunata mutane uku.
Mutumin, mai suna Christian Ganczarski na tsare ne a gidan yarin bayan da aka yanke masa hukuncin shekaru 18 a gidan yari, bisa alaka da wani hari da ya yi sanadiyyar hallaka mutane 21 a shekara ta 2002.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu