Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya sanya hannu kan sabuwar dokar yaki da ta’addanci

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanya hannu kan sabuwar dokar yaki da ta’addancin kasar wadda za ta bai wa hukumomi damar shiga gidajen jama’a domin gudanar da bincike, da kuma rufe wuraren ibada kana da hana wadanda ake zargi tafiye-tafiye.

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Dokar wadda ta maye gurbin dokar ta bacin da aka saka bayan harin birnin Paris na shekara ta 2015, a watan jiya ta samu amincewar Majalisar Dokokin kasar .

Shugaba Macron ya ce sabuwar dokar da za ta fara aiki daga gobe laraba 1 ga watan Nowamba 2017 zata taimaka wajen kare lafiyar 'yan kasar.

Faransa dai na daga cikin kasashen turai da hare-haren ta’addanci ya haifarwa salwantar rayukan mutane da dama a shekaru 2 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.