Isa ga babban shafi
Amurka-Venezuela

Maduro ya sha alwashin sanya kafar wando guda da Amurka

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro, yayi gargadin cewa, kasarsa zata daina saidawa Amurka man fetur, sakamakon sabon takunkumin karya tattalin arzikin da ta kakabawa gwamnatinsa.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro yayin gabatar da jawabi a babban birnin kasar Caracas.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro yayin gabatar da jawabi a babban birnin kasar Caracas. REUTERS/Marco Bello
Talla

Maduro ya yi gargadin ne, yayin da yake Alla wadai da matakin gwamnatin Amurka na kakabawa Venezuela takunkumi, a kafar talabijin din kasar, wadda ya bayyana a matsayin tsabar mugunta.

Karkashin sabon takunkumin, gwamnatin Trump, ta haramtawa Venezuelan gudanar da huldar cinikayya da kasashen waje.

To sai dai Maduro, ya ce babu wata barazana da zata sanya Venezuela, bada kai ga wata kasa da ke neman yi mata katsalandan, zalika ya yi gargadin cewa, sabon takunkumin zai shafi ayyukan Amurkawan da ke aiki a kasar, da kuma hannayen jarin da kamfanonin Amurka suka zuba a kasar ta Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.