Faransa
Faransa Ta Shirya Zaben Wakilan Majalisar Dokoki na Lahadi
Gobe Lahadi ne al’ummar kasar Faransa ke yin zaben wakilan majalisar kasar karkashin sabon Shugaban kasa Emmanuel Macron
Wallafawa ranar:
Talla
Zaben zai kasance zagaye na farko ne, inda sabon Shugaban ke fatan samun rinjayen wakilai a majalisar kasar.
Nasarar da ya samu a watan jiya ya haifarda sabon salo a siyasar Faransa kuma jam'iyar sa na fatan ganin sun sami rinjayen wakilai a majalisa don su sami aiwatar da manufofinsu ba tare da jibin goshi ba.
Akwai kujeru 577 da suka hada da na wakilai ‘yan kasar Faransa dake zaune a wajen kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu