Isa ga babban shafi
Birtaniya

Musulmi zai zama magajin garin London

Yau mazauna birnin London na Birtaniya ke zaben magajin gari, zaben da a karon farko ke nuna cewar za a zabi musulmi mai suna Sadiq Khan a karkashin jam'iyyar Laboour duk da suka da bata sunan da yake fuskanta daga 'yan adawa, cikin su, har da firaminista David Cameron.

Sadiq Khan, musulmi na farko da ake sa ran zai zama magajin gari a birnin London na Birtaniya
Sadiq Khan, musulmi na farko da ake sa ran zai zama magajin gari a birnin London na Birtaniya REUTERS/Toby Melville
Talla

Wata kuri'ar jin ra'ayi da aka gudanar ta nuna cewa, Sadiq Khan wanda mahaifinsa dan asalin kasar Pakistan ne, na iya kasancewa musulmi na farko da zai rike mukamin magajin garin wani birnin a kasashen Turai

Ko a jiya Laraba, bayan gudanar da zazzafan yakin neman zabe, bincike ya nuna cewa, Khan wanda mahaifinsa direban Tasi ne, na gaban dan takarar jam’iyyar Conservative Zac Goldsmith da maki 14.

Khan wanda wasu ke yi masa mummunan zato, ya nesanta kan sa daga jita-jitar kyamatar yahudawa, sannan ya kare kan sa daga caccakar da Goldsmith ya yi ma sa na rashin cewa uffam dangane da ra’ayin rikau da wasu musulmai ke nunawa.

Khan mai shekaru 45 ya girma ne a tsakanin talakawa kuma ya yi aiki a matsayin lauya mai kare hakkin dan adam, kafin daga bisani ya rike kujerar ministan gwamnatin Birtaniya.

Shi kuwa, abokin hamayyarsa, Goldsmith mai shekaru 41, dan marigayin attajirin nan ne James Goldsmith, kuma mai gwagwarmayar kare muhalli ne, sannan kuma dan majalisar dokoki ne karkashin jam’iyyar Consevative.

A hirar da ya yi da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, Sadiq Khan ya ce, shi, mutumin birnin London ne, kuma dan asalin Birtaniya ne, sannan shi musulmi ne, kuma yana alfahari da haka.

A fannin kwallon kafa kuwa, Khan ya ce, shi mai goyon bayan kungiyar Liverpool ne.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.