Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan sanda su yi arangama da dalibai a Faransa

‘Yan sanda a birnin Paris na kasar Faransa sun yi arangama da gungun wasu dalibai kimanin dubu biyar da ke zanga zangar adawa da sauye sauyen dokar kwadago na gwamnatin kasar.

Jami'an tsaron Faransa na kokarin kashe wutar da dalibai suka cinna wa wata mota a lokacin zanga zangar ta ranar Alhamis.
Jami'an tsaron Faransa na kokarin kashe wutar da dalibai suka cinna wa wata mota a lokacin zanga zangar ta ranar Alhamis. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Sai da jami’an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla kafin su tarwatsa gangamin yayin da kuma daliban suka raunata ‘yan sanda da dama  a lokacin zanga zangar ta ranar Alhamis.

Dandazon daliban dai sun fantsama ne a titunan birnin Paris, inda suka rika rera wakokin nuna adawa da shirin gwamnatin na sauye dokar kwadago kafin daga bisani zanga zangar ta nemi rikidewa zuwa tarzoma a lokacin da daliban suka fara farfasa motocin jama’a.

Ganin haka ne, ya sa 'yan sandan kwantar da tarzoma suka shiga aikin tarwatsa daliban, abinda ya yi sanadin jikkatar wasu ‘yan sandan.

Tuni dai aka cafke fiye da 30 daga cikin daliban.

Majalisar zartarwar Faransa dai ta amince da sauye sauyen duk da sukar da tsarin ya sha tun da fari.

Shugaban kasar Francois Hollande na neman a sake zaben sa  a wa’adi na biyu, amma wasu na ganin daukar irin wannan mataki ka iya kawo ma sa tarnaki.

Dubban matasa da wadanda ke kammala karatu a Faransa na yin aiki ne na gajeren wa’adi a kasar, ko kuma aiki irin na sha ka tafi, yayin da suke bukatar samun aiki na dahir.

Wata kididdigar jin ra’ayi na baya bayan nan, ta nuna cewa kashi 58 na Faransawa ne ke adawa da sabon tsarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.