Faransa
Matuka jiragen ruwa na zanga zanga a Faransa
Daruruwan matuka jigaren ruwa sun rufe hanyoyi a birnin Calais, inda suke amfani da tayoyi masu cin wuta, don hana jama’a isa gabar ruwan birnin.
Wallafawa ranar:
Talla
Kimanin ma’aikata 300, dake aiki a kamfanin Scop SeaFrance na kasar ta Faransa ne ke nuna adawa da matakan da ake shirin dauka, na sayar da jiragen kamfanin ga wani na kasar Denmark.
Ko a farkon wannan watan sai da ma’aikatan suka yi irin wannan zanga zangar, inda suka rufe hanyoyin garin tsawon kwanaki 3 a jere.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu