Isa ga babban shafi
Faransa

Areva zai sayar wa EDF da bangarensa na Nukiliya

Kamfanin Areva mai hakar ma’andinin Uranium ya amince ya siyar da hannayen jarinsa a bangarensa na Nukiliya ga kamfanin wutar lantarki na EDF.

Ginin Kamfanin hakar ma'adinin Uranium na Areva a Faransa
Ginin Kamfanin hakar ma'adinin Uranium na Areva a Faransa AFP PHOTO BERTRAND GUAY
Talla

A wata sanar da kamfanin na EDF mai samar da wutar lantarki ya fitar, ta bayyana cewa tun a ranar 30 ga watan Yunin ne Areva ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar.

A karkashin yarjejeniyar EDF zai sayi tsakanin kashi 51 zuwa 75 cikin 100 na wani sashin injin sarrafa makamashin Nukliya na Areva akan kudaden da yawansu ya kai Yuro biliyan 2 da miliyan 700 wanda ya yi dai dai da dalar Amurka Biliyan 3.3
Shugaban kamfanin EDF Jean Bernerd Levy ya ce,

An tuntubi wadansu kamafanonin dabam game da siyan sauran hannayen jarin na Areva, yayin da tsohon Shugaban kamfanin siminti na Swiss, Bernerd Fontana ya amince da jan ragamar shugabancin kamfanin Areva.

Sai dai kudaden da aka sqayi hannayen jarin ba su kai yuro biliyan 4 ba da ya bukata a farko, amma zasu taimaka masa wajan samar da euro biliyan 7 da ya ce yana bukata nan da shekara ta 2017 domin inganta harkokinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.