Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun ceto daruruwan mutane daga hannun Boko Haram

Sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka wani adadin mayakan Boko Haram, yayin farmakin da suka kai musu a tsakanin yankunan Jakana da Mainok dake kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno.

Wasu dakarun sojin Najeriya.
Wasu dakarun sojin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Babban Jami’in hulda da manema labaran rundunar sojin Najeriyar, Kanal Aminu Ilyasu, ya ce yayin samamen tsakanin ranakun Juma’a zuwa asabar, 3 zuwa 4 ga Janairun 2020, sojojin sun yi nasarar ceto jimillar mutane 461 daga hannun mayakan na Boko Haram.

Wadanda aka ceton kuma sun hada da mata 154, kananan yara 207 da kuma maza 100.

Sanarwar rundunar sojin Najeriyar ta kuma bayyana ceto wasu kananan yara 4, daga hannun mayakan na Boko Haram akan hanyar Damasak zuwa Kareto dake karamar hukumar Mobbar a jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.