Dakarun Najeriya sun kame manyan kwamandojin Boko Haram
Rundunar sojin Najeriya tace dakarunta sun kame wasu mayakan Boko Haram 16 a yankin Pulka dake karamar hukumar Gwoza.
Wallafawa ranar:
Dakarun Najeriyar sun kai samamen ne a ranar 20 gawatan Oktoban 2019, inda suka kame mayakan, ciki har da wasu manyan kwamandojin kungiyar ta Boko Haram da ke cikin jerin wadanda ake nema ruwa a jallo.
Mai magana da yawun sojojin Najeriya Kanal Aminu Iliyasu, ya ce kwamandojin masu tada kayar bayan da suka shiga hannu sun hada da Lawan Abubakar Garliga, mutum na 41 da kuma Bayaga Manye na 90, dukkaninsu da ke cikin manyan jagororin kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo.
Kakakin sojin Najeriyar Kanal Iliyasu, ya ce binciken farko da suka gudanar, ya nuna cewa, wasu daga cikin mayakan da suka kama, na cikin wadanda suka kai kazaman hare-hare a Pulka da Gwoza, sai kuma yiwa wasu jami’an ‘yan sanda kisan gilla a shekarun baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu