Isa ga babban shafi

Boko Haram ta fuskanci koma baya mafi muni cikin watanni 6 - MNJTF

Rundunar sojin hadin gwiwar kasashen yammancin Afrika masu fama da matsalolin tsaro MNJTF, ta ce mayakan Boko Haram da a yanzu ke kiran kansu da ISWAP sun fuskanci koma baya mafi muni cikin watanni shidda.

Wasu sojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa.
Wasu sojin Jamhuriyar Nijar a yankin Diffa. Warren Strobel/Reuters
Talla

Kakakin rundunar hadin gwiwar ta MNJTF Kanal Timothy Antigha, yace a ci gaba da shirinsu mai taken 'Operation Yancin Tafki', na murkushe Boko Haram, a ranar Juma’a sun halaka mayakan 42, tare da kwace tarin makamai, yayin farmakin da suka kai musu a Doron Naira, wani tsibirin Yankin Tafkin Chadi.

Daga cikin makaman da sojin suka kwace akwai motoci biyu masu dauke da manyan bindigogi masuaman wuta, da kuma bindigogin AK 47 15.

Kanal Antigha ya ce yayin artabun, sun rasa soja daya, wasu 10 kuma sun jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.