Isa ga babban shafi
Najeriya

Amurka, Birtaniya da EU sun yi tsokaci kan dakatar da Onnoghen

Bangarori da dama a ciki da wajen Najeriya, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan matakin shugaban kasar Muhammadu Buhari, na dakatar da Alkalin Alkalai mai shari’a Walter Onnoghen.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP/Audu MARTE
Talla

Kungiyar Tarayyar Turai, Amurka da Birtaniya sun bayyana damuwa kan matakin na dakatar da Onnoghen, wanda ake zargi da kin bayyana wasu makudan kudaden kasar waje da ya mallaka a asusunsa, kamar yadda dokar da’ar ma’aikata a Najeriya ta tanada.

Kungiyar tarayyar Turai EU, kira tayi ga gwamnatin Najeriya da kuma ‘yan adawa, su bi tsarin doka, wajen warware takaddamar da matakin dakatar da Alkalin Alkalan ya haifar.

A nata bangaren, Amurka ta ce ta damu da matakin ne, la’akari da cewa, an sauya alkalin alkalan, ba tare da hadin gwiwar bangaren majalisar dokokin kasar ba. Yayinda Birtaniya ta ce matakin zai iya shafar sahihancin zabukan kasar na 2019 da za’a yi nan da makwanni kalilan, inda tace bai kamata a dauki matakin a irin wannan lokaci ba.

Tuni dai dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya Atiku Abubakar, ya dakatar da yakin neman zabensa tsawon kwanaki uku, domin nuna adawa da matakin dakatar da mai shari’a Onnoghen daga mukaminsa.

Sai dai yayin bangarori da dama ke maida martanin goyon baya ko akasin haka kan batun dakatar da alkalin alkalan, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce dakatar da Onnoghen ya biyo bayan umarnin kotun kasar ta da’ar ma’aikata, wadda ta ce za a tantance makomarsa bayan kammala yi masa shari’a kan laifin kin bayyana wasu kadarori da ya mallaka.

Zalika, shugaba Buhari, ya ce kamata yayi tun da fari, mai shari’a Onnoghen, ya saukakawa kowa wajen yin murabus bisa radin kansa, la’akari da cewa, shi da kansa a rubuce, ya amince da aikata laifin kin bayyana wasu kadarorin nasa, abinda ya daganta da kuskure da kuma mantuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.