Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kalubalanci 'yan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kalubalanci al’ummar kasar da suka hada ga kungiyoyi da su gabatar da wata kwakkwarar shaidar da ke nuna cewa, mambobin majalisar ministocinsa na da laifin cin hanci da rashawa a kansu, yayin da shugaban ya lashi takobin daukar mataki nan take muddin aka tabbatar da gaskiyar zargin.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari REUTERS/Dan Kitwood
Talla

Buhari ya kalubalancin ‘yan kasar ne a yayin wata hira a karkashin shirin “The Candidates” da aka watsa kai tsaye a kafar talabijin din gwamnatin kasar a ranar Laraba da daddare.

Shugaban ya bayyana haka a yayin amsa tambayoyi kan zargin gwamnatinsa da karkatar da akalar yaki da cin hanci da rashawa kan wasu tsirarun mutane a Najeriya, yayin da ta ke kawar da kanta daga tuhumar ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki da ake zargin su.

Mai gabatar da shirin na “The Candidate”, Kadariya Ahmed ta bada misali da tsohon sakataren gwamnatin kasar, Babachir Lawal da aka sallama saboda almundahana, amma ba a gurfanar da shi ba, hasali ma, an gan shi yana yi wa Buhari yakin neman zabe.

A yayin bayar da amsa, shugaba Buahri ya ce, babu adalci a cikin wannan sukar da ake yi wa gwamnatinsa, domin kuwa har yanzu maganarsa na gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, kuma an bayar da umarnin tuhumar sa da dukkanin wadanda ake zargin su da aikata irin laifinsa a cewar Buhari.

A bangare guda, shugaba Buhari ya bayyana cewa, zai amince da sakamakon zaben 2019 duk da dai ya ce, yana da kwarin guiwar samun nasara.

Shirin na "The Candidates" wanda gidauniyar MacArthur ta shirya, na tattaunawa ne da 'yan takara a zaben 2019 da mataimakansu domin jin manufofinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.