Sama da mutane dubu 2 sun rasa rayukansu a Zamfara
Akalla mutane sama da 2,000 suka rasa rayukansu sakamakon bala’in satar shanun da ya addabi jihar Zamfara da ke Najeriya a cikin shekarun baya-bayan nan.
Wallafawa ranar:
A baya-bayan nan mutane sama da 40 aka kashe a biranen da ke karamar hukumar Zurmi, kafin daga bisani aka yi nasarar hallaka shugaban kungiyar masu satar shannun da suka addabi jihar da ake kira Buharin Daji.
Bashir Ibrahim Idris da ya ziyarci jihar ta Zamfara, a hada mana rahoto kan rikicin da ke addabar jihar
Rahoto kan rikicin satar shanu a Zamfara
Karamar hukumar Zurmi na Arewa da birnin Gusau da ke jihar Zamfara, kuma yanki ne na manoma da makiyaya da kuma 'yan kasuwa, yayin da rashin samun cikakken tsaro daga hukumomi ya tilasta wa mazauna yankin nemawa kansu matakan kariya daga 'yan bindigar da ke hallaka jama'arsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu