Isa ga babban shafi

'Yan kunar bakin wake sun hallaka mutane 5 a Maiduguri

Wasu ‘yan kunar bakin wake guda biyu, sun kai hari kan sansanin ‘yan gudun hijira dake Dalori a garin Maiduguri, dake arewa maso gabashin Najeriya a yammacin jiya.

Jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, tare da wasu mayakansa.
Jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, tare da wasu mayakansa. © AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Wakilinmu a Maiduguri Bilyaminu Yusuf, ya rawaito cewa daya dan kunar bakin waken ya tada bam din jikinsa ne waje kuma nesa da sansanin ‘yan gudun hijirar, inda ya hallaka kansa.

Daya dan kunar bakin waken kuma ya kutsa cikin sansanin ‘yan gudun hijirar inda ya hallaka akalla mutane 5 da kuma jikkata wasu da dama.

Shugaban hukumar agajin gaggawa na Jihar Ahmed Satomi ya tabbatar da kai harin.

Makwanni biyu da su gabata akalla mutane 12 suka hallaka, wasu kimanin 50 suka jikkata, a harin da wasu ‘yan kunar bakin wake biyu suka kai a garejin Muna da ke birnin Maiduguri.

Tun bayan murkushe karfin kungiyar Boko Haram da rundunar sojin Najeriya ta yi, masu tada kayar bayan sun mayar da hankali wajen amfani da hare-haren kunar bakin wake domin hallaka mutane a yankin arewa maso gabashin Najeriya, musamman a garin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.