Isa ga babban shafi
Najeriya

Fiye da Mutane 14 Boko Haram ta kashe a harin masallacin Gamboru

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari wani masallaci tare da hallaka akalla mutane 14 baya ga jikkata da dama. Harin na zuwa ne kwana guda bayan gwamnatin Borno da hadin gwiwar jami'an tsaro sun sanar da sanya dokar takaita zirga-zirga don kawo karshen hare-haren baya-bayan nan da kungiyar ta kai yayin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara. 

Hare-haren dai na ci gaba da kazanta a dai dai lokacin da mahukuntan jihar ke kara tsananta matakai don kawo karshensu.
Hare-haren dai na ci gaba da kazanta a dai dai lokacin da mahukuntan jihar ke kara tsananta matakai don kawo karshensu. STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Wasu bayanai sun ruwaito guda cikin mayakan sa kai na Kato da gora da ke aikin bayar da kariya ga jama'a na cewa harin ya faru ne da misalin karfe 5 na asubahi dai dai lokacin da mutane ke sallah.

Umar Kachall daya daga cikin mayakan na sa kai ya ce maharan sun ruguza masallacin tare da jikkata mutane da dama bayan wadanda suka Mutu.

Ko a jiya ma sai da kungiyar ta Boko Haram ta kai wani harin kunar bakin wake a wata kasuwa da ke garin Biu na Maiduguri da ya hallaka mutane 15 baya ga jikkata fiye da 50.

A cewar rundunar ‘Yansandan jihar wasu mata ne daure da bom jikinsu suka dirarwa kasuwar inda daya ta tayar da bom a cikin kasuwar yayinda dayar ta tayar a wajen kasuwar.

Hare-haren dai na ci gaba da kazanta a baya-bayan nan duk da matakan da ake ci gaba da dauka na sanya dokar takaita zirga-zirga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.