Isa ga babban shafi
Najeriya

An harbe dan wasan Shooting Stars a Neja Delta

An harbe wani dan wasan kwallon kafa a yankin Neja Delta na Najeriya wanda ke buga gasar Firimiya a kasar. Rahotanni sun ce Sojojin kasar ne da ke fada da tsagerun yankin bisa kuskure suka harbe dan wasan mai suna Izu Joseph da ke buga wa kungiyar Shooting Stars wasa.

Dan wasan Shooting Stars Izu Joseph da sojoji suka kashe a Neja Delta
Dan wasan Shooting Stars Izu Joseph da sojoji suka kashe a Neja Delta goal.com
Talla

Wasu rahotanni sun ce an harbe dan wasan ne a wani yankin da sojoji suka kai farmaki kan masu tayar da kayar baya a Neja Delta.

Dan wasan dai ya buga wasan da Shooting Stars ta yi kunnen doki ci 1 da 1 da kungiyar Rangers da ta lashe kofin Firimiya a bana.

Babu dai wata sanarwa daga rundunar Sojin Najeriya.

Kungiyar marubuta labarin wasanni a Najeriya ta danganta rasuwar dan wasan a matsayin babban rashi, tare da yin kira ga gwamnati ta dauki matakan da suka dace domin kaucewa sake aukuwar haka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.