Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Najeriya na alhinin rashin Amodu Shu'aibu

‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana alhini kan mutuwar tsohon mai horar da tawagar kwallon kafar kasar, Amodu Shu'aibu, wanda ya rasu a cikin daren da ya gabata yana da shekaru 58 da haihuwa.

Marigayi Amodu Shuaibu
Marigayi Amodu Shuaibu NFF
Talla

Gabanin rasuwar dai, marigayin ya koka da ciwon kirji da ke damunsa kamar yadda hukumar kwallon kafar Najeriya ta shaida wa manema labarai.

Rasuwarsa na zuwa ne, a yayin da ‘yan kasar ke ci gaba da alhinin mutuwar Stephen Keshi, wanda shi ma tsohon kocin tawagar Super Eagles ne da ya rasu yana da shekaru 54 da haihuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.