Isa ga babban shafi
Najeriya

Hare haren bama-bamai sun kashe mutane a Yobe

Akalla mutane 17 sun rasa rayukansu sakamakon wasu jerin a hare haren kunar bakin wake da aka kaddamar a sanyin safiyar yau laraba a jihar Yobe dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kungiyar Boko Haram ta sha kaddamar da hare hare a jihar Yobe.
Kungiyar Boko Haram ta sha kaddamar da hare hare a jihar Yobe. (Photo : Reuters)
Talla

An dai kai harin fako ne a wani shago dake rukunnan gidaje na BUHARI ESTATE, inda mutane biyar suka mutu nan take yayin da aka kai hari na biyu a kusa da wani masallaci dake cikin rukunnan gidajen, inda mutane biyu su ka riga mu gidan gaskiya.

Kana mutane 10 su ma sun rasa rayukansu a hari na uku wanda aka kai a wata rugar Fulani dake kusa da gabashin Ma’aikatar ayyuaka ta jihar Yobe.

A hirarsa da RFI hausa, babban Jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA a jihar Yobe, Bashir Idris Garga ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya kara da cewa tuni suka kwashe gawarwakin mutawan da suka mutu a hare haren, wadanda kuma suka samu raunuka na samun kula wa a asibiti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.