An nemi MDD ta gindaya 2030 a matsayin shekarar da za a kawo karshen talauci a duniya
Shugabannin kasashen Indonesia, Liberia da kuma Firaministan Birtaniya, sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta ayyana shekara ta 2030 idan Allah ya kai mu a matsayin shekarar da za a kawo karshen talauci a duniya baki daya.
Wallafawa ranar:
Shugaban Indonesia Susilo Bambang, da shugaban Liberia Ellen Johnson Sirleaf da kuma Firaministan Birtaniya David Cameron, sun bayyana cewa akwai bukatar Majalisar ta samar da wani shiri da zai kawo karshen talauci da kuma samar da daidaito a tsakanin al’ummar duniya kafin shekarar ta 2030.
A daidai lokacin da Shirin Cimma Muradun Karni na MDD ya dogara a kan batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da kuma yaki da talauci.
Shugabannin kasashen uku sun ce akwai bukatar Majalisar ta sanya batun rikice-rikice, da yake-yaken basasa, samar da kyakkyawan jagoranci da kuma yaki da rashawa a matsayin manyan ginshikai da za su kai ga samar da nasarar cimma wani buri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu