Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Sochaux ta doke Lyon da ci 2-1

Lyon ta yi kasa a gwiwa a kokarinta na ganin ta lashe kofin gasar bayan ta yi mamaya a hanun Sochaux da ci 2-1.  Hakan kuma ya bar Lyon a matsayi na uku da maki 53, wato da tazarar maki 8 ke nan tsakaninta da Paris Saint Germaine wacce ita kuma ta doke Montepllier da ci 1-0, wanda ya ba PSG damar samun cigaba da jagorantar teburin gasar da maki 61. Marseille wacce ta doke Nice da 1-0 na biye ne da ita da maki 54. 

Lokacin da Lyon ke karawa a wani wasanta
Lokacin da Lyon ke karawa a wani wasanta REUTERS/Robert Pratta
Talla

Wasa tsakanin Ajjacio da Toulous an ta shi ne da ci 3-2, inda Ajjacio ta samu nasara akan Toulous, kana Bordeaux da Lorient suka tashi da ci 1-1 a yayin daTroyes da Saint -Etienne suma suka ta shi da ci 2-2. Lille kuwa ta bi Brest har gida ne ta doke ta da ci 2-1.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.