Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Lyon ta yi kunnen doki da Brest da ci 1-1

Lyon ta ga samu ta ga rashi yayin da ta tashi a wasanta da Brest da ci 1-1, wanda hakan ya hana ta samun damar doke Paris Saint Germain a gasar French League, wannan ya kuma faru ne a dai dai lokacin da Marseille, wato daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafar da ke gaba-gaba a gasar ta doke Troyes da ci 2-1. A yanzu haka dai PSG na matsayi na daya da maki 54, Lyon kuwa na matsayi na biyu da maki 52 kana Marseille na matsayi na uku da maki 49.  

Dan wasan Lyon bayan karawarsu a wani wasa
Dan wasan Lyon bayan karawarsu a wani wasa REUTERS/Philippe Laurenson
Talla

Sauran sakamakon wasannin da aka kara a karshen gasar ta French League na nuna cewa, Lille ta doke Bordeaux da ci 2-1, ita kuwa Reims ta lallasa PSG da ci 1-0, kana Nice ta sha kayi a hanun Saint - Etienne da ci 4-0.

Lorient da Valenciennes sun ta shi ne suma da kunnen doki da ci 1-1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.